Bayanin Haƙƙin Mallaka

Yin amfani da rubutu, hotuna da sauran abin cikin wannan rukunin yanar gizo yana ƙarƙashin waɗannan sharuɗɗa da yanayi da ke biyowa.

Abin da ke ciki na ƙarƙashin kariyar dokokin mallakar ilimi

Fayilolin rubutu da hotuna, murya da bidiyo, da sauran abin da ke cikin wannan rukunin yanar gizon mallakar DEREK PRINCE MINISTRIES-INTL INC ne (nan gaba za a kira shi 'Derek Prince Ministries'). Haƙƙoƙin mallaka da sauran haƙƙoƙin mallakar abin da ke cikin wannan rukunin yanar gizon na iya kasancewa mallakar wasu mutane ko ƙungiyoyi waɗanda ba Derek Prince Ministries ba. Derek Prince Ministries ta hana kwatanta duk wani abu mai kariya a wannan rukunin yanar gizon, sai dai don amfanin da ya dace kamar yadda aka ayyana a cikin dokar mallaka, kuma kamar yadda aka bayyana a nan ƙasa.

An Bada Izinin yin Amfani da ya dace

Yin amfani da ya dace na kayan da aka mallaka ya haɗa da amfani da kayan da aka kiyaye ba domin dalilan kasuwanci ba, misali koyarwa, tallafi, yin bincike, suka, sharhi, da kuma rahoton labarai. Sai dai idan an faɗi wani abu na daban, masu amfani da suke son sauke ko buga fayilolin rubutu da hotuna daga wannan rukunin yanar gizo don irin wannan amfani, za su iya yin haka ba tare da izini na musamman daga Derek Prince Ministries ba, matuƙar sun cika waɗannan sharuɗɗa na nan ƙasa:

  1. Ana iya amfani da abin da ke cikin ne kawai don kanka, don karin ilimi ko dalilai waɗanda ba na kasuwanci ba;
  2. Dole masu amfani su ambaci marubucin da kuma asalin abin da ke ciki kamar yadda za su yi da kayan buga kowane irin aiki;
  3. Dole ambaton ya haɗa da duk bayanan mallakar haƙƙi da sauran bayanan da ke da alaƙa da abin da ke ciki da URL na rukunin yanar gizon Derek Prince Ministries;
  4. Ba za a canza ko gyara wani abin da ke ciki ba;
  5. Dole masu amfani su bi duk sauran sharuɗɗa ko ƙa'ídodin da aka ƙayyade waɗanda za su iya shafar fayil fayil, hoto, ko rubutu.

Garanti

Ta wurin saukarwa, bugawa, ko kuma amfani da fayilolin rubutu da hotuna daga wannan rukunin yanar gizo, masu amfani sun yarda kuma sun tabbatar da cewa za su iyakance amfani da irin waɗannan fayilolin don amfani da ya dace kuma za su cika duk sauran sharuɗɗa da ƙa'ɨdodin wannan lasin, kuma ba za su keta haƙƙin Derek Prince Ministries ko wani mutum ko ƙungiya ba. Derek Prince Ministries ba zai tabbatar da cewa amfani da rubutu, hotuna da abin da ke cikin da aka nuna a rukunin yanar gizon ba zai keta haƙƙoƙin wasu ƙungiyoyi waɗanda ba su da mallaka ko dangantaka da Derek Prince Ministries ba.

An hana yin Amfani don Kasuwanci

Bugawa don kasuwanci ko amfani da rubutu, hotuna ko abin da ke cikin wannan rukunin yanar gizo ba tare da izini ba an hana shi. Duk wanda ke son yin amfani da ɗaya daga cikin waɗannan fayilolin ko hotuna don yin kasuwanci, bugawa, ko kuma wani dalili ba domin amfani kamar yadda aka ayyana ta doka ba, dole ne ya nema kuma ya karɓi izinin a rubuce daga Derek Prince Ministries. An ba da izini kaɗai don irin wannan amfani bisa matsayin yanayi na daban daban bisa ga ra'ayin Derek Prince Ministries. Ana iya cajin kuɗi don yin amfani amma ya danganta ne bisa ga nau'i da yanayin amfani da aka shirya.

Akwai Tambayoyi?

A tuntuɓe mu idan kuna da ƙarin tambayoyi dangane da wannan Bayanin Haƙƙin Mallaka.

A Tuntuɓe Mu