Kalmomi 30 masu ƙarfi
Kowace magana tana ƙunshe da sunan littafi ko wa'azi.

“Addu’a ba ta da iyaka. Ita ce babbar makamin yaƙin mu mai kaiwa nesa. Za mu iya jefa ta daga ko’ina kuma mu sa ta kai ko’ina.”
Fallasa Shaiɗan
“Ruhu Mai Tsarki ya san hanya domin Shi ne ya tsara taswirar.”
Za ku karɓi iko
“Daga zuciya ne al’amuran rayuwa ke fitowa. Lokacin da dokar Allah take cikin zuciyarka, kana rayuwa ta hanyar Allah.”
Za ku karɓi iko
“Babu wani abu kamar rabin biyayya.”
Ƙofar samun albarkar Allah
“Mutumin da ya miƙa kansa ga Allah yana duba komai yadda Allah ya ke dubansa.”
Ƙofar samun albarkar Allah
Ilimi yana sanya mabuɗin a hannunka, amma bangaskiya ce ke juya mabuɗin a ƙofar kuma ya buɗe ɗakin taskar wadatar Allah a cikin Almasihu.”
Shaida

“Ina ganin idan akwai abu guda da ya fi wuyar karba a wurin Allah, shi ne yabo da rabin zuciya.”
Shiga gaban Allah
“Kowane Mai bi yana da wani fasali na hikimar Allah da zai bayyana wa duniya, kuma yana bayyana ta ne ta wurin shaidar rayuwar sa.”
Shafuka daga littafin rayuwata
“Bisa ga tsarin Allah, aure alkawari ne inda kowane ɗayan su yake sadaukar da rayuwarsa domin ɗayan, sannan su yi zaman sabuwar rayuwa da juna.”
Abokan Rayuwa
“Addu’a cewa ‘MulkinKa shi zo’ yana nufin sadaukarwa ga daidaituwa da duk abin da ya shafi zuwan mulkin.”
Sake gano Ikklisiyar Allah
“Babbar matsalarmu a matsayin mu na ’yan adam ita ce ba mu fahimci yadda muke da daraja ba.”
Dokokin Aiki
“Kada ka ƙaskantar da kanka, domin Allah yana ɗaukar ka da dajara. Ya bada jinin Yesu dominka.”
Manufar yin Gwaji
“Allah har yanzu yana ji da kyau. Yin tuba da watsar da zunubanmu yana sake buɗe hanya zuwa gare Shi.”
Za ku karɓi iko

“Ra’ayin da ake da shi game da aure a kowace al’ada ko wayewa, yawanci alama ce ta gaskiya da ke bayyana ainihin ɗabi’u da yanayin ruhaniya.”
Allah Mai Haɗa Aure ne
“Yin naciya, hanya ce ta musamman, ta samun abu mafi kyau na Allah.”
Karɓar Abu Mafi Kyau daga wurin Allah
“Darasin shi ne: dole ka kasance mai shirin barin komai. Babu adalci, babu ma’ana, zalunci ne! To sai me? Allah ne ya shirya shi haka. Shi ne mai iko. Wannan ita ce bangaskiya!”
Alherin Mika wuya
“Rayuwar Krista ba kawai jin daɗi da kiɗan goge ba ce. Duk wani Krista da ya miƙa kansa zai ga cewa yaƙi na cikin abin da zai ɗanɗana a rayuwarsa.”
Yaƙi a Cikin Sama
“Ɓata 'ya'yan ku ba alheri ba ne. Sau da dama, babu shakka, alamar ragwanci ce. Yafi sauki a lalatar da 'ya'ya da a horar da su.”
Mazaje da Ubanni
“Wacce ce hanyar shiga hutu? Jin muryar Allah. Wannan shi ya sa muke da Krista masu damuwa da yawa. Ba su san yadda za su ji muryar Allah ba.”
Ku Kula da Kanku (Sashi na 1)
“Ƙwayar maganar: shaida. Sa'ad da Yesu ya mutu, na mutu. Sa'ad da aka binne Shi, aka binne ni. Sa'ad da ya tashi, na tashi. Gaskata cewa na karɓi adalci daga wurin Allah ta wurin bangaskiya.”
Tafiya zuwa Roma

“Yesu ne mai bambanta ruhun ɗan adam. Makomarsu ta har abada ta danganta ne da wurin da su ka tsaya da Yesu.”
Ƙarshen Rayuwa
“Akwai abubuwa uku da dole ka yi don karɓar baftismar Ruhun Mai Tsarki: ka ji ƙishi, ka zo wurin Yesu, ka sha.”
Za ku karɓi iko
“Kowanne lokaci da ka yanke shawara mai kyau, kana ƙarfafa ɗabi'a mai kyau kuma kana gina hali mai kyau.”
Za ku karɓi iko
“Na gaskata cewa yana da muhimmanci ƙwarai a gare mu duka mu gane cewa zunubi na farko a duniya ba kisa ba ne, ba zina ba ne, amma girman kai ne.”
Yaƙi a cikin Sama
“Bai kamata mu bar abubuwan da ba mu gane ba su toshe mana wuraren sanin gaskiya inda Allah ya bayar da fahimta mai kyau.”
Yaƙi a cikin Sama
“Ba za mu iya kasancewa na Allah ba idan ba mu kasance a shirye domin bauta masa ba. Allah ba ya marabtar lalatattu masu son kai a gidansa.”
Yaƙi a cikin Sama
“Daukar giciye na nufin mika son zuciyar mu.”
Ƙofa zuwa albarkar Allah

“Halin ka game da kuɗi a gaskiya yana bayyana halin ka game da Allah da kansa.”
Shirin Allah domin Kuɗinka
“Bangaskiyar ƙwarai ta Littafi Mai Tsarki tana fitowa daga zuciya kuma ta na nuna yadda rayuwar mu take. Ba kawai wani ilimin kai ba ne, ko kuma nishaɗin zuci; amma ainihin wani ƙarfi ne mai aiki a cikin zuciya.”
Bangaskiya ta yin Rayuwa
“Halin da muka haɓakar a cikin wannan rayuwa shi zai ƙayyade yadda za mu kasance a har abada. Wata rana za mu bar baye bayen mu a baya; halinmu zai kasance tare da mu har abada.”
Bagaskiya ta Yin Rayuwa