Tarihi
Komai ya fara ne a shekara ta 1971 lokacin da Derek Prince ya buɗe ma'aikata a cikin garejin gidansa a Fort Lauderdale, Florida. Da farko dai an san ta da suna Derek Prince Publications, sakamakon ci gaban da hidimar Koyaswarsa ta Littafi Mai Tsarki ta samu, wadda ta faro a shekara ta 1944 lokacin da Ubangiji ya ce masa:
An kira ka don ka zama malamin Nassi, cikin gaskiya da bangaskiya da kuma ƙauna, wadanda suke cikin Almasihu Yesu - ga mutane da yawa.''
Waɗannan kalmomi ne suka ƙarfafa ƙoƙarin Derek na ciyar da waɗanda suke jin yunwar ruhaniya, suna ba shi ƙarfin gwiwa ya rubuta kuma ya wallafa littattafai da dama ciki har da "Nazarin Littafi Mai Tsarki don kan ka" (1969), "Gaskiya Mai 'Yantarwa" (1966), " Ka Tuba ka Bada Gaskiya" (1966) da sauran su. Wannan ya zama shaida ga nasarar waɗannan littattafai da amincin Allah, buƙatar Derek Prince Publications kuma ta ƙaru.
A shekara ta 1972, aikin wallafawa ya fi ƙarfin Derek shi kaɗai, sai da aka gayyaci David Selby (surukin sa) ya taimaka. Tare suka tsara hanya ga wannan hidima mai girma, suna amfani da gidan rediyo da kuma wallafa sabbin littattafai.
An buɗe ofisoshi a ƙasashen New Zealand, Afirka ta Kudu, Australia, Canada, Birtaniya da Netherlands a cikin shekaru na 1980 zuwa 1989 , kuma burin almajirantar da al'ummai ya tabbata. Zuwa ƙarshen wannan lokacin, Derek ya kammala tafiyar koyar da Littafi Mai Tsarki sau uku a faɗin duniya, kuma an yada shirin rediyonsa cikin duniya a harsunan ƙasashe goma.
A shekara ta 1990, an sake sunan Derek Prince Publications zuwa Derek Prince Ministries. Rarraba kayan koyarwa na Littafi Mai Tsarki kyauta ya ƙara ƙarfi, yana kaiwa ƙasashe 140 gaba ɗaya, kuma littattafan Derek sun kasance a cikin harsuna fiye da 50.
A yau, Derek Prince Ministries yana da ofisoshi a ƙasashe fiye da 45 a faɗin duniya kuma ya bada kansa gaba ɗaya wajen ƙoƙarin koyar da Littafi Mai Tsarki a kowace ƙasa, kabilu da harsuna. Ci gaba da kuma nasarar hidima ta tabbatar da kalmar annabci da Derek ya samu a shekara ta 1941, lokacin da Ubangiji ya ce:
“Zai zama kamar ƙanƙanin rafi. Rafin zai zama kogi. Kogin zai zama babban kogi. Babban kogin zai zama teku. Tekun zai zama babban teku, zai kasance ta wurin ka. Amma ta yaya? ba za ka sani ba, ba lallai ka iya sani ba, ba za ka sani ba."
Amincin Allah ga wannan Kalmar shi ne ya kawo Derek Prince Ministries inda ta ke a yau, kuma zai ci gaba da kai hidimar zuwa cikin "babban teku mai girma."
Tare da ɗimbin kayan rubutu, sauti, da bidiyo na Derek Prince, ma'aikatar tana ci gaba da wallafa sabbin littattafai. Zuwa yau, an wallafa littattafai fiye da 100 kuma an fassara su cikin harsuna fiye da 100.