Tambayoyi da aka fi yawan yi game da Derek prince

Shahararren Malamin koyarda Littafi Mai Tsarki zuwa ga Al'ummai, Derek Prince mutumin Allah ne wanda ake girmamawa sosai saboda fahimtar sa ta Littafi MaiTsarki da hikimar sa wurin Koyaswa

Abubuwan da ke ciki

Danna don zuwa wurin

A ina aka haifi Derek Prince?

Bangalore, India

Yaushe aka haifi Derek Prince?

14 ga watan Augusta 1915

Derek Prince ya mutu?

Derek Prince ya rasu ran 24 ga watan Satumba 2003

Derek Prince ya rasu da shekara nawa?

Shekara 88 (1915 - 2003)

A ina Derek Prince ya rasu?

Derek Prince ya rasu a gidansa a kasar Urushalima

A ina aka binne Derek Prince?

A Makabartar Ekklesiayar Alliance Church International, Urushalima

Ta Yaya Derek Prince ya mutu?

Derek Prince ya rasu ne a barchin sa saboda gazawar zuciya bayan wani dogon lokaci na rashin lafiya

Menene Derek Prince yayi imani da shi?

Derek Prince baya cikin wani tsari ko wata kungiya ta musamman amma Krista ne wanda ya yi Imani da Baftismar Ruhu Mai Tsarki. Imaninsa daidai ya ke da imanin mu, wanda ke bi da mu a dukkan al'amuran imani da aikawa

Bayanin Bangaskiya
Wani lokaci mutane sukan tambaye ni, ''wacce Ikklisiya ka ce zuwa? Ni kan so amsawa kamar Maizabura: ' Ina abota da duk masu tsoron Allah, da duk masu bin dokokin sa.'' Ba batun suna ba ne; batun halin zuciya ne da kuma yadda muke rayuwa''

Wane fassarar Littafi MaiTsarki Derek yafi so?

Derek ya fi son Fassarar nan da ake kira King James Version. Har ma ya karanci ainihin rubutun asali na Ibraniyanci da Helenanci

Domin bada bayani a sarari ga masu sauraro, ya na ywan amfani da fassarori na zamani irin su New American Standard Bible(Sabuwar Fassara ta Amurka), New International Version(Sabuwar Fassara ta Duniya), New King James Version (Sabuwar Fassara ta King James Version). Wani lokaci kuma yana amfani da Litafi Mai Tsari wanda J.B. Philips ya juyaya, The Living Bible(Wato Littafi Mai Tsarki Na Rayuwa), ko Fassarar Amplified Bible, idan sun fi bayyan ma'anar batun da kyau

Derek Prince ya taba aure?

Derek ya yi aure da zaman gwauranci sau biyu

Lydia Prince
Aure: 1946 - 1975

Ruth Prince
Aure: 1978 - 1998
Na yi aure da Lydia tsawon shekaru 30, da Ruth kuma shekaru 20. Dukansu sun kasance auren farin ciki da nasara.'' Derel Prince

Yaushe Lydia Prince ta rasu?

5 ga watan Oktoba, 1975 (shekaru 85)

Yaushe Ruth Prince ta rasu?

29 ga watan Disamba 1998 (shekaru 68)

Derek Prince yana 'ya'ya?

Marigayi Derek Prince mahaifi ne ga yara 12